’Yan Sanda sun maida dan kasar Sin da ke nema gida kan safarar Rosewood tun 2021

Police repatriate Chinese ‘fugitive wanted since 2021 over rosewood smuggling 750x430

Hukumar ’Yan Sandan Najeriya ta sanar da cewa ta mika Zhang Shijie, wani dan kasar Sin da ake nema a kasarsa kan zargin safarar kimanin tan 1,400 na nau’in itacen Rosewood na African wanda ke fuskantar barazanar karewa.

Jami’an hukumar INTERPOL ta kasa (NCB) da ke Abuja ne suka kama Zhang a ranar 10 ga Satumban 2026, a yankin Ogere da ke Jihar Ogun.

Rundunar ’yan sandan ta bayyana cewa, Hukumar Yaki da Fasa-kwauri ta Haikou a kasar Sin ce ke neman wanda ake zargin ruwa a jallo, sakamakon zarginsa da hannu a safarar itacen Pterocarpus erinaceus, wanda aka fi sani da African rosewood.

A cewar wata sanarwa da Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Najeriya, Ani Iniedu ya fitar a ranar Alhamis, an bayar da sammacin kama Zhang ne tun ranar 7 ga Janairu, 2021.

Hukumar ta ce an aikata laifukan ne a tsakanin watan Nuwamba 2020 da Janairu 2021, inda aka yi safarar itacen mai nauyin tan 1,400, wanda darajarsa ta kai kusan yuan miliyan 15.7 na kasar Sin.

“Sakamakon dabarun tattara bayanan sirri, sanya idanu da kuma hadin gwiwar bincike, jami’an INTERPOL NCB na Abuja sun kama wanda ake zargin a ranar 10 ga Satumba, 2026, a yankin Ogere na Jihar Ogun.”

’Yan sandan sun kara da cewa Zhang ya gudu daga kasar Sin bayan tafka laifin, inda aka gano cewa yana zaune ne a Jihar Ogun da ke Najeriya.

A lokacin da aka kama shi, an same shi da fasfo din kasar Sin wanda wa’adinsa ya riga ya kare tun ranar 11 ga Nuwamban 2023.
Hukumar ta ce an mayar da Zhang birnin Guangzhou na kasar Sin ranar Laraba, 16 ga Satumban 2026, karkashin yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin ‘yan sandan kasashen biyu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here