Tinubu ya yaba da hukuncin ICC na yin watsi da ikirarin dalar Amurka miliyan 680 na kamfanin Sunrise Power

Bola Tinubu Tinubu aaaaaaaaaaa 700x430

Shugaba Bola Tinubu ya yaba da hukuncin Kotun Kasuwanci ta Duniya (ICC) wanda ya yi watsi da ikirarin neman diyyar dalar Amurka miliyan 680 da kamfanin Sunrise Power and Transmission Company Ltd ya shigar a kan Najeriya.

Tinubu ya bayyana wannan hukunci a matsayin gagarumar nasara ga Najeriya, kuma wani babban mataki na kawar da cikas na shari’a da ya kawo cikas ga aikin samar da wutar lantarki na Mambilla.

Kotun sasancin ta kasa da kasa da ke karKashin ICC a birnin Paris ta yanke wannan hukunci ne a ranar Alhamis.

Shugaban ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu a ranar Alhamis a birnin Abuja.

Kamfanin Sunrise ya bukaci dalar Amurka miliyan 680 a matsayin sulhu da ruwa a kan wata shari’a da ta shafi ikirarinsa na neman fiye da dalar Amurka biliyan 2.7.

Wannan babban ikirari ta shafi takaddamar da ke da alaka da gina aikin samar da wutar lantarki ta Mambilla mai karfin megawatt 3,960 a jihar Taraba.

Tinubu ya ce hukuncin ya tabbatar da kudurin Najeriya na kare muradunta da abin da ya bayyana a matsayin ikirari na zalunci da cin zarafi.

“A madadin Gwamnati da Al’ummar Tarayyar Najeriya, ina mai jinjina wa gagarumin kokarin Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari’a, Prince Lateef Fagbemi da daukacin tawagar Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya saboda kokarinsu a kan wannan lamari,” in ji shi.
Shugaban ya kuma yaba wa tawagar lauyoyin da suka kare Najeriya karkashin jagorancin Ms Elizabeth Oger Gross da Mista Tolu Obamuroh na Paul Hastings LLP.

“Ina kuma jinjina wa tawagar lauyoyin kare martabar Najeriya (FRN), karkashin jagorancin Ms Elizabeth Oger Gross da Mista Tolu Obamuroh, duka biyu na Paul Hastings LLP, saboda kwarewarsu da kuma kyakkyawar kariya da suka yi wa kasar nan,” in ji Tinubu.

Ya kuma yaba wa tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo da marigayi Shugaba Muhammadu Buhari saboda kishin kasa da goyon bayan da suka bayar, inda ya bayyana cewa duka biyun sun bayar da shaida a shari’ar.

Tinubu ya ce takaddamar ta samo asali ne tun daga kan kwangilar shekarar 2003 na gina tashar wutar lantarki mai karfin megawatt 3,050 a jihar Taraba karkashin tsarin build-operate-transfer.

Ya bayyana cewa Majalisar Zartarwa ta Tarayya ba ta amince da wannan kwangilar ba.

Shugaban ya kuma yaba wa tsoffin ministoci Babatunde Fashola da Suleiman Adamu da sauran shaidu da masana.

Ya yaba wa gudummawar da suka bayar wajen kare muradin Najeriya a lokacin sasancin.

Bugu da kari, Tinubu ya yaba wa Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro saboda goyon bayansa da hukumar yaki da yi wa tattalin arziki ta’annati (EFCC) saboda binciken da ta gudanar a kan lamarin.

Shugaban ya tabbatar da cewa Najeriya za ta ci gaba da kasancewa mai aminci wajen hadaka da sahihan masu zuba jari da kuma mutunta yarjejeniyoyin shari’a.

Sai dai ya ce kasar za ta ci gaba da kare kanta da duk wani ikirari na neman cin zarafi a kan dukiyoyin al’ummarta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here