Ministan cikin gida, Olubunmi Tunji Ojo, ya ba da umarnin dakatar da kwamandan hukumar tsaro NSCDC na Jihar Neja, Suberu Aniviye, nan take biyo bayan mutuwar wasu da ake zargi masu hakar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba ne a jihar.
Ministan ya kuma ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin, wanda rahotanni suka ce ya auku ne a yankin M.I. Wushishi/Lukoto da ke Minna, babban birnin jihar, a cikin sa’o’in farko na ranar Alhamis.
Read also: Hajj 2025: NAHCON da hukumar jin dadin alhazai ta jiha sun tsayar da ranar fara jigilar Maniyyata.
Wannan matakin na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban mai taimaka wa ministan kan kafafen yada labarai da hulda da jama’a, Alao Babatunde, ya fitar a ranar Jumma’a.
Bayanin sanarwar ya bayyana cewa, an kama mutanen da ake zargin masu hakar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba ne yayin wani samamen tabbatar da bin doka da aka gudanar a sassan Jihar Neja a ranakun 15 and 16 ga watan Satumban 2026.
“Wannan abu ne mai ban takaici, sai dai za a gudanar da cikakken bincike yayin da kwamandan da abin ya faru a karkashin kulawarsa zai kasance an dakatar da shi.
“Muna gudanar da gwamnati ce wadda babban fifikonta shi ne tsaron rayuka, kuma mun yi aiki don tabbatar da hakan,” in ji ministan.
Read also: An Dage Karan Hadi Sirika Da Dan Uwan Bisa Rashin Halartar Kotu
Tunji-Ojo ya bukaci jam’a da su kwantar da hankalinsu kuma su kasance masu bin doka domin ba da damar gudanar da bincike na gaskiya.
Haka kuma ya jajantawa Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago da kuma iyalai da dangin mamatan.
Rahotanni sun bayyana cewa adadin mutanen da ake zargi masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba da suka mutu a tsare ya kai 37, yayin da ita kuma hukumar NSCDC ba ta bayyana takamaiman adadi ba.
Tun da farko, mutuwar ta sanya hukumar NSCDC kafa wata tawagar bincike domin gano ainihin abubuwan da suka haddasa aukuwar lamarin.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, Jami’in Hulda da Jama’a na NSCDC na Ƙasa, Babawale Afolabi, ya ce tawagar, wadda Mataimakin Kwamandan Janar mai kula da Leken Asiri da Bincike ke jagoranta, an ba ta umarnin gudanar da bincike na tsanaki.
Read also: Kotu ta wanke tsohon minista Turaki daga zargin karkatar da kudade
Binciken zai shafi yanayin da ake tsare da mutanen a lokacin da aka kama su, lokacin da suka yi a tsare, yanayin wurin da aka tsare su, kulawar likita da aka ba su, da sauran dukkan wasu abubuwan dake kewaye da mutuwar tasu.
Hukumar ta NSCDC ta kuma yi gargaɗi game da yin hasashe a kan abin da ya yi sanadiyyar mutuwar tasu, inda ta ce rahotannin da ke alakanta mutuwar da wata cuta na bukatar tabbatarwa daga likitoci da gwajin dakin bincike.












































