Taron mahaddata Kur’ani: Sarkin Musulmi ya sanar da dalilan ɗage taron

d6764bb9 ee43 48f7 9b16 7874af898bf5 e1663538043755

Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta harkokin Addinin Musulunci ta kasa (NSCIA), Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya tabbatar da dage taron mahaddata Alkur’ani mai girma da aka shirya yi a ranar 22 ga Fabrairu, 2025.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a daren Juma’a mai dauke da sa hannun Farfesa Is-haq Oloyede, babban sakatare na NSCIA.

Sultan a cikin sanarwar ya kuma bayyana wasu dalilan da suka sa aka dage taron.

Karin karatu: Hukumar USAID ce ke tallafa wa Boko Haram da sauran kungiyoyin ta’addanci – dan majalisar dokokin Amurka

Sanarwar ta ce, daya daga cikin dalilan da aka lissafa shi ne sama da mutane dubu 500,000 ne ke da sha’awar halartar taron da aka shirya tun farko a filin wasa na MKO Abiola da ke Abuja.

Sarkin Musulmi ya ce za a sanar da sabon ranar da za a gudanar da taron bayan watan Ramadan na bana, wanda ake sa ran za a fara a watan Maris mai zuwa.

Wannan ci gaban dai na zuwa ne kasa da mako biyu gabanin gabatar da taron, wanda ake sa ran za a ga sama da malamai 30,000 mahaddata Alkur’ani da marubuta a fadin kasar nan a Abuja.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here