Sojoji sun sanar da karɓe mulki a Guinea-Bissau

tGbissauPoliticsElectionUnrest
Brigadier General Denis N'Canha (C), head of the military office of the presidency gives a press conference at the General Staff of the Armed Forces on November 26, 2025. Gunfire was heard Wednesday outside Guinea-Bissau's presidential palace just three days after the country's presidential and legislative elections, with both major candidates have claimed victory, an AFP journalist on the scene witnessed. People were seen running in a crowd gathered outside the palace as the shots were heard. (Photo by Patrick MEINHARDT / AFP)

Jami’an sojin Guinea-Bissau sun sanar da karɓe ikon ƙasar gaba ɗaya tare da dakatar da dukkanin tsarin zaɓe da kuma rufe iyakokin ƙasar.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki uku bayan gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ’yan majalisa a ƙasar mai fama da talauci da rikice-rikice.

Tun da safiyar ranar Laraba aka fara jin harbe-harbe a kusa da fadar shugaban ƙasa, wadda dama ƙasar ta sha fama da juyin mulki.

Mazauna yankin sun riƙa rugawa da gudu bayan ganin sojojin da suka mamaye babbar hanyar da ke kaiwa fadar gwamnati.

Daga bisani jami’an sojin sun karanta wata sanarwa a hedikwatar rundunar soji da ke babban birnin ƙasar, Bissau, suna bayyana cewa sun ɗauki ikon ƙasar baki ɗaya tare da kawo karshen duk wani mataki na ci gaba da tsarin zaɓe, kamar yadda wakilan jaridar AFP suka gani.

Karin bayani na nan tafe…..

AFP

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here