A ranar Asabar 3 ga watan Mayu ne mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima zai bar Abuja zuwa birnin Libreville na kasar Gabon domin wakiltar Najeriya a wajen bikin rantsar da zababben shugaban kasar, Brice Nguema.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Shettima zai halarci taron ne a madadin shugaban kasa Bola Tinubu.
Kakakin mataimakin shugaban kasar, Mista Stanley Nkwocha, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa, ya ce Najeriya na ci gaba da goyon bayan sauyin dimokradiyya cikin lumana a Gabon.
Nkwocha ya kuma tabbatar da babbar manufar gwamnatin Najeriya na inganta mulkin dimokaradiyya da kwanciyar hankali a yankin Afirka ta tsakiya.
Karin karatu: Zargin badaƙalai: EFCC ta fara binciken Mele Kyari, da wasu manyan jami’an NNPC
Ya ce ana sa ran mataimakin shugaban kasar zai dawo Najeriya bayan an rantsar da shugaban kasar.
NAN ta ruwaito cewa Nguema, wanda ya rike mukamin shugaban rikon kwarya na Gabon tun watan Agustan 2023, ya samu gagarumar nasara a zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 12 ga Afrilu.
Bisa sakamakon karshe da kotun tsarin mulkin kasar Gabon ta fitar, Oligui Nguema ya samu kuri’u 58,074 – kwatankwacin kashi 94.85 na kuri’un da aka kada.
Oligui Nguema dai ya fuskanci ‘yan takara bakwai a zaben da suka hada da tsohon Firaminista Alain Claude Bilie-By-Nze wanda ya zo na biyu da kashi uku cikin dari na kuri’un da aka kada.
Sauran ‘yan takarar sun kasa zarce kashi 1 cikin dari. (NAN)