Tsohon Sanatan mazaɓar Zamfara ta tsakiya, Kabiru Garba Marafa, wanda ya taɓa riƙe mukamin Kodinetan yakin neman zaɓen Tinubu/Shettima na jihar Zamfara a zaben shugaɓen shekarar 2023, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC.
Marafa, wanda ya wakilci Zamfara ta tsakiya a majalisar dattawa daga shekarar 2011 zuwa 2019, ya ce, ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar ne saboda salon shugabancin shugaba Bola Tinubu.
Matakin dai ya biyo bayan taron kwana biyu da kungiyar tuntuba ta Sanata Kabiru Marafa ta yi, wanda ya samu magoya baya daga dukkanin ƙananan hukumomi 14 na jihar Zamfara.
Taron wanda aka gudanar a Kaduna a ranakun 27 da 28 ga watan nan da muke ciki na Agusta, ya tattauna ne kan matsalolin tsaro da siyasa da ci gaban jihar Zamfara.
A karshen taron, kungiyar ta fitar da sanarwa mai dauke da sa hannun shugabanta, Kwamared Bashir Muhammad Mafara da sakatarenta Dakta Mannir Bature Tsafe da sauran mambobi da dama.
Sanarwar ta bayyana cewa, a karkashin jagorancin Marafa, Shugaba Tinubu ya lashe zaben shugaban kasa na 2023 a Zamfara.
A lokacin yakin neman zaben, Marafa ya tabbatar wa Tinubu cewa babu bukatar ziyartar Zamfara, domin zai kai kuri’un jihar, alkawarin da kuma ya cika shi.
Sai dai kungiyar ta nuna takaicin cewa duk da wannan biyayya da gudunmawar, jihar Zamfara ta yi zargin rashin kulawa da ita a gwamnatin Tinubu.












































