Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta kama wasu ƙasurguman ‘yan bindiga 2 a jihar Taraba tare da ƙwace babura daga hannunsu.
Wata sanarwa da mataimakin kakakin runudunar, Kanal Oni Olubodunde, ya fitar ta ce dakarun rundunar Operation Whirl Stroke ne suka yi nasarar kama mutanen da ba ta bayyana sunansu ba a ranar Alhamis.
“Samamen da dakarun suka kai bayan tattara bayanan sirri a ƙauyen Geshi na ƙaramar hukumar Donga a jihar Taraba ya yi sanadiyyar ƙwato babur biyu da ‘yan ta’addan ke amfani da su,” in ji sanarwar.
Karin labari: Chima Udoye ya lashe gasar Nigerian Idol na shekarar bana
Ta ƙara da cewa, “an samu bayanan sirrin ne bayan wasu mahara sun kai hari, inda dakaru suka ɗunguma zuwa Geshi kuma suka fara musayar wuta da su abin da ya sa suka tsere zuwa cikin daji.
“Yanzu haka ‘yan ta’addan na hannunmu domin gudanar da bincike” a cewar sanarwar, kamar yadda BBC Hausa ta wallafa.