Jami’an tsaro hudu sun rasa rayukansu a sabon kwanton-bauna da ‘yan ta’adda suka kai wa jami’an tsaro a arewa maso gabashin jihar Borno, kamar yadda Daraktan Hulɗa da Jama’a na rundunar Soji mai rikon mukamin, Laftanar Kanar Appolonia Anele, ya bayyana a ranar Asabar.
Dakarun suna karkashin rundunar Ayyuka ta Musamman ta 25, yayin da suke sintiri domin kare al’ummomi a yankin Wajiroko da ke Azir Multe, ƙaramar hukumar Damboa ta jihar Borno, sun gamu da harin ba-zata daga ‘yan ta’adda yayin da suke dawowa daga wani nasarar sintiri a gefen dajin Sambisa.
Tawagar sintirin, ƙarƙashin jagorancin Kwamandan Rundunar 25 Birgediya Janar M. Uba, wanda ya haɗa dakaru 25 da mambobin ƙungiyar hadin gwiwa ta Civilian Joint Task Force, ta yi luguden wuta da ƙarfin hali har ta tilasta wa maharan ja-da-baya ba tare da cimma manufarsu ba.
Sai dai, a yayin wannan harin, “sojoji biyu masu jarumta da mambobin Civilian Joint Task Force biyu masu ƙwazo sun rasa rayukansu yayin aikin hidimar ƙasa.”
Karanta: Rundunar sojin Najeriya ta musanta sace kwamandan rundunar a jihar Borno
Shugabancin rundunar soji ya yaba da jarumtakar dakarun, tare da mika ta’aziyya ga iyalai da abokan wadanda suka mutu saboda sadaukarwarsu ga ƙasa.
Wannan lamari ya biyo bayan tabbacin babban hafsan rundunar saman ƙasa, Air Marshal Kelvin Aneke, ranar Juma’a, na cewa rundunar saman Najeriya tana ci gaba da jajircewa wajen kare ƙasa da kawar da ‘yan ta’adda, masu tada ƙayar baya, da sauran masu aikata laifuka da ke barazanar zaman lafiya da tsaro.
Air Marshal Aneke ya bayar da wannan tabbacin ne yayin ziyarar aiki da ya kai wa Rundunar Saman Operation FANSAN YAMMA, Sector 2/213 Forward Operating Base, da ke Katsina.













































