Jam’iyyar PDP ta kori tsohon gwamnan jihar Rivers kuma ministan Abuja, Nyesom Wike, da sakataren bangaren ayyukan jam’iyyar, Samuel Anyanwu, da kuma tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, bisa zargin cin amanar jam’iyyar.
Jam’iyyar ta amince da wannan kudiri ne a taron ta na ƙasa da ke gudana a Ibadan, inda ɗaya daga cikin manyan Dattawa jam’iyyar, Cheif Bode George, ya gabatar da shi, gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, kuma ya mara masa baya cikin cikakkiyar amincewa.
Wasu da aka yanke hukuncin korarsu sun haɗa da lauyan jam’iyyar, Adeyemi Ajibade, Umar Bature, Abdulrahman Mohammed, Mao Chuambuwa, George Turner, Austin Nwachukwu, Abraham Ammah da Dan Orbih.
Karin labari: Ibadan: Damagum, Bala Mohammed, Makinde da wasu sun karɓi tutoci a yayin fara babban taron ƙasa na jam’iyyar PDP
Jam’iyyar ta ce korar ta zama dole domin tabbatar da hukunta masu karya dokokin jam’iyya da kuma mai da ita kan turbar da take bi tun asalinta.
Jami’an jam’iyyar da ke jagorantar taron ƙasa sun bayyana cewa an zartar da hukuncin ne bayan gudanar da cikakken nazari kan ire-iren ayyukan da ake zarginsu da aikatawa.
A Ibadan, wurin taron ya kasance tattare da wakilai daga jihohi daban-daban da suka hallara domin karɓar sabbin matsaya da kuma tabbatar da sabbin tsare-tsaren shugabanci.
Jam’iyyar PDP ta ce za ta ci gaba da ɗaukar matakan ladabtarwa ga duk wanda ya yi karya ko ya saɓawa manufar jam’iyya domin tabbatar da dorewar haɗin kai da bin doka a tsarinta.













































