Jam’iyyar NNPP, ta yaba wa hukumar INEC da jami’an tsaro bisa tabbatar da sahihin zaɓe a mazabar Shanono/Bagwai da Ghari a jihar Kano.
Sakataren yada Labarai na NNPP na kasa, Ladipo Johnson, ne ya bayyana hakan a ranar Asabar a Abuja, inda ya kuma yaba wa al’ummar Kano bisa yadda suka ba da gudunmawa wajen kada kuri’a bisa tsari na gaskiya a lokacin zaben na cike gurbi.
Sai dai ya yi Allah wadai da kiran da aka yi na soke zabukan biyu.
Johnson ya bayyana kiran da aka yi na soke zaben, wanda ake zargin an samu tashin hankali, wanda mai magana da yawun jam’iyyar APC Felix Morka ya buƙaci a soke zaben.
Ya ci gaba da cewa, a buƙatar Morka bai nuna ainihin abubuwan da suka faru ba, ya na mai jaddada cewa, dan takarar jam’iyyar NNPP ya yi nasara da gagarumin rinjaye, kamar yadda INEC ta bayyana.
Johnson ya bayyana cewa, an gudanar da zabukan mazabu biyu na gaskiya, kuma mai sahihanci da zaman lafiya, ya kara da cewa a matsayin jam’iyyar NNPP da ke da karfi, ba za a iya samun sakamakon ba.
Ya kara da cewa Kano ta ci gaba da zama a matsayin jihar magoya bayan jam’iyyar NNPP, wanda hakan ya sa ba za a iya tunanin APC za ta iya yin nasara ba, domin tarihin zabe da sakamakon da aka samu a ‘yan kwanakin nan ya nuna akasin haka.
Ya yaba wa al’ummar Kano kan yadda suka bijire wa munanan ayyuka a lokacin zabe, inda ya kara da cewa hukumar zabe ta INEC da kuma ‘yan sandan Kano sun tabbatar da sahihancin zaben wanda ya gudana cikin kwanciyar hankali ba tare da tashin hankali ba.
NAN













































