Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) da kuma kungiyar TUC sun bayyana rashin jin dadinsu bisa kin fara biyan mafi karancin albashi dubu N30,000 ga ma’aikatan jihar zamfara.
Hakan na konshe cikin wata sanarwa da kungiyoyin biyu suka fitar, ta hannnu sakatarorin su Mista Ahmed Abubakar na NLC da kuma Sani Kwotorkwoshi na TUC, ranar Alhamis a Gusau.
Sanarwar ta bayyana ciwa duk alamomi sun nuna gwamnatin zamfara bata da niyar fara biyan mafi karancin albashin.
Kungiyoyin biyu sun nemi membobin su da suyi hakuri kan lamarin, kuma kongiyoyin zasu cigaba da bin duk wasu hanyoyi don ganin gwamnatin ta fara biyan mafi karancin albashin.
A wani bangaren kuma gamayyar kongiyoyin sun yabawa gwamnatin jahar ta Zamfara bisa kokarinta na yawan karawa ma’aikata girma da take.
(NAN)













































