NDLEA ta kama kayan maye da aka ɓoye cikin ƙwaryar Dodon Kodi da Ƙwayayen fitilu a filin jirgi na Lagos

imgonline com ua twotoone tcRHFHGkN8gItgOK 750x430

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta ƙasa (NDLEA), ta kama wasu kunshe-kunshen miyagun ƙwayoyi da aka ɓoye cikin ƙwaryar Dodon Kodi da kuma fitilu masu cajin lantarki a filin jirgin sama na Murtala Muhammed a Legas.

Kayan mayen ana yunkurin fita da su ƙasashen Amurka, Biritaniya da Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo.

Rahoton hukumar ya bayyana cewa an kama mutane biyu da ake zargi da hannu a yunkurin fitar da kayan, ciki har da wani jami’in jigila mai suna Boladale Riliwan wanda aka cafke ranar 7 ga Oktoba 2025 bayan an gano kunshin ƙwayar skunk guda 15 da aka ɓoye a cikin fitilu goma da aka shirya tura wa Congo.

Haka kuma, an kama wata mata mai suna Olawale Oyebola Hakeemot, mai shekaru 48 da haihuwa, wadda ke aiki a fannin kiwon lafiya a Biritaniya, a ranar 12 ga Oktoba yayin da take shirin tafiya birnin Manchester ta jirgin Qatar Airways inda aka gano tana ɗauke da ƙwaryar Dodon Koɗi da aka ɓoye a cikinsu ƙwayoyin tramadol guda 2,300.

A wani samame daban, jami’an NDLEA sun hana wata ƙungiya fitar da ƙwayoyin bromazepam guda 810 da aka ɓoye cikin kayan mata zuwa Amurka ta wani kamfanin jigila a Legas.

A jihar Adamawa kuwa, an kama wani mai suna Bello Buba a Namtari, karamar hukumar Yola ta Kudu, da ƙwayoyi 38,270 na tramadol da aka ɓoye cikin motarsa daga Jamhuriyar Benin.

Hukumar ta kuma lalata gonar skunk mai girman hekta 21.3 a Ilawe, jihar Ekiti, inda ta ƙone kayan maye nauyin kilo 53,250 tare da kama mutane uku da ake zargi.

Haka nan a Ondo, an lalata hekta 6.96 na irin wannan tsirrai da nauyin su ya kai kilo 17,400.

A wasu jihohin da suka haɗa da Oyo, Ogun, Imo, Enugu da Legas, hukumar ta kama ƙarin mutane da dama da kuma miyagun ƙwayoyi masu tarin yawa, ciki har da kwalaben magani irin su codeine kimanin 80,000 da aka gano a cikin kwantena daga ƙasar Indiya a tashar jiragen ruwa ta Apapa.

Wannan mataki na NDLEA ya nuna ci gaba da jajircewar hukumar wajen hana safarar miyagun ƙwayoyi da yaɗuwarsu a cikin ƙasar da ma wajen ƙasashen waje.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here