Shugaban Uganda mai ci, kuma ɗan takarar jam’iyyar National Resistance Movement, Yoweri Museveni, ya sake lashe saɓe a wa’adi na Bakwai a shugabancin ƙasar bayan zaɓen da ya gudana a ranar Asabar, wanda ya samu rahotannin tashin hankali da kuma katsewar internet a faɗin ƙasar.
Hukumar zaɓe ta Uganda ta bayyana cewa Museveni mai shekaru 81 ya samu kashi 71.65 na ƙuri’un da aka kaɗa, a zaɓen da aka gudanar a ranar Alhamis, yayin da aka samu rahotannin mutuwar aƙalla mutane 10 tare da tsoratarwa da matsin lamba ga ’yan adawa da ƙungiyoyin fararen hula.
Wannan nasara ta bai wa Museveni damar tsawaita mulkinsa zuwa shekaru 40 a matsayin shugaban ƙasar da ke Gabashin Afirka, inda ya doke Bobi Wine mai shekaru 43, tsohon mawaki da ya koma siyasa, wanda ya samu kashi 24.72 na ƙuri’un zaɓen.
Bobi Wine ya shiga wasan ɓuya bayan jami’an tsaro sun kai samame gidansa, lamarin da ya sa ya bayyana kin amincewarsa da sakamakon zaɓen baki ɗaya, tare da nuna cewa jami’an tsaro na neman cafke shi yayin da matarsa da wasu ’yan uwansa ke tsare a gida.
Tuni dai aka samar da tsauraran matakan tsaro a babban birnin Kampala, inda jami’an tsaro ke ƙoƙarin hana barkewar zanga-zanga irin wadda ta faru a ƙasashen Kenya da Tanzania a ’yan watannin baya, yayin da ’yan sanda suka musanta kai samame gidan Bobi Wine, suna mai cewa sun taƙaita zirga-zirga ne a wuraren da suka ɗauka a matsayin masu haɗarin tsaro.
Masu sa ido kan zaɓe daga Afirka sun nuna cewa ba su ga hujjar cuɗanya ƙuri’u ba, amma sun yi tir da rahotannin tsoratarwa, kama mutane da sace-sace da aka ce an yi wa ’yan adawa da ƙungiyoyin fararen hula, lamarin da tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce ya haifar da tsoro da kuma raunana amincewar jama’a da tsarin zaɓe.
Jam’iyyar National Resistance Movement mai mulki ta Museveni ta samu rinjaye a kujerun majalisar dokoki bisa sakamakon wucin gadi, yayin da masu sharhi ke kallon zaɓen a matsayin abin da aka riga aka kammala tun da Museveni ke da cikakken iko da tsarin mulki da na tsaro, tare da murƙushe duk wani ƙalubale a tsawon mulkinsa.













































