Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙaƙaba takunkumin hana mallakar makamai da yin tafiye-tafiye da ƙwace dukiyoyin jagororin ‘ƴan tawaye shida da ke Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo daidai lokacin da ake rikici a gabashin ƙasar.
Cikin waɗanda takunkumin ya shafa har da kakakin ƙungiyar ‘ƴan tawaye ta M23 da soja mai muƙamin janar da ke ƙarƙashin ƙungiyar FDLR sai wasu manyan jagororin ƙungiyar ADF.
Karanta wannan: IGP ya gargadi rundunar ‘Yan Sandan Najeriya
Sauran sun haɗa da shugaban gamayyar ƙungiyar kare ‘ƴancin al’ummar Congo da kuma wani kwamanda na ƙungiyar Twirwaneho.
Sanarwar ta biyo bayan taron kwamitin tsaro na MDD na ranar Talata wanda aka yi domin tattauna taɓarɓarewar tsaro a Congo.
Karanta wannan: Za’a fara hukunta yaran da ba sa zuwa makaranta a Kano – Ma’aikatar Ilimi
Congo na zargin Rwanda da marawa kungiyar M23 baya yayin da gwamnatin Rwanda ta zargi maƙwabciyarta da haɗa ai da ƴan tawayen FDLR da ta ce tana da alaƙa da kisan kiyashin da aka yi na 1994.
Yayin taron kwamitin tsaron, mambobi sun yi ta yin Allah-wadai da harin da M23 ta kai a baya-bayan nan a garin Sake abin da ya ɗaiɗaita dubban mutane.