Shugaban kasa mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya mika sakon ta’aziyar tsohon Ministan Kwadago kuma tsohon Sakataren Gwamnatin Kano, Alhaji Musa Gwadabe da ya rasu bayan gajeriyar jinya.
Sakon ta’aziyar na kunshe cikin wata sanarwa da Abdulaziz Abdulaziz ya sawa hannu a yau Laraba. Margayun ya rasu ne yana da shekaru 87 a duniya.
Tinubun ya bayyana rasuwar Gwadabe a matsin babban rashe wanda zai yi wuya a cikin gurbin shi.













































