Magatakardan Jami’ar BUK Ya Rasu

Jamil Salim 750x430 1
Jamil Salim 750x430 1

Magatakardan Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) Farfesa Jamilu Ahmad Salim ya rasu.

A safiyar Laraba aka gudanar da jana’izarsa a masallacin Juma’a da ke sabuwar harabar jami’ar da ke titin zuwa Gwarzo.

Kafin rasuwarsa dai shi ne magatakardar BUK tun daga shekarar 2021, bayan maye gurbin Hajiya Fatima Bint Muhammad da ta shafe shekaru biyar kan matsayin.

An haife shi a ranar 21 ga watan Nuwamba a 1963 a unguwar Gwale da ke Kano, kuma ya kammala digirinsa na farko a Fannin Hausa/Islamic Studies a shekarar 1988.

Haka kuma ya yi babbar Difloma (Post graduate) a fannin Siyasa da Gudanarwa da kuma digirinsa na biyu a fannin Kasuwanci da Dokoki duk a Jami’ar Bayero ta Kano.Farfesa Salim ya fara aiki da BUK a shekarar 1990, kuma ya shafe shekaru tara kafin komawa aiki da Hukumar Shirya Jarabawar (NECO) a 1999 inda ya shekara daya, sannan ya sake dawowa aiki da jami’ar a shekarar 2000.

Hakazalika ya yi aiki a bangarorin jamiar da dama kafin zamowarsa magatakardan jamiar a watan Oktoban 2021.
Da fatan Allah Ya ji kan sa, Ya kuma yi masa rahama. Amin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here