Majalisar wakilai ta bukaci NAFDAC ta sanya ido kan masu siyar da magunguna ta yanar gizo

DFFF7859 C882 4F5A B6A6 27DC0F2CB7F2
DFFF7859 C882 4F5A B6A6 27DC0F2CB7F2

Majalisar wakilai ta bukaci hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) da ta sanya ido ayyukan masu talla da sayar da magunguna ta yanar gizo a Najeriya.

Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin da dan majalisa Onofiok Luke (PDP-Akwa-Ibom) ya gabatar a ranar Talata a Abuja.

Da yake gabatar da kudirin, Luka ya ce akwai bukatar su sanya ido kan masu tallace-tallacen a yanar gizo da masu siyar da kwayoyi, saboda suna isar da sakonnin tallace-tallace ga al’umma da yawa.

Luka ya bayyana cewa yana da kyau a fito da tsari da zai  shawo kan matsalar siye da siyarwar magunguna da kwayoyi ba bisa ka’ida ba.

Ya ce tallace-tallacen yanar gizo ya kara zama muhimmin abu ga masu kasuwanci da masu a duniya saboda saukin gudanarwa.

Dan majalisar ya kara da cewa masu sayar da magungunan ta yanar gizo suna  amfani da damar shiga yanar gizo kyauta da kuma shafukan sada zumunta don tallata da sayar da magungunan da ba a yi wa rajista ba.

Ya ja hankalin ‘yan Najeriya wajen siyan magungunan da suka hada da kayan abinci, magungunan rage cholesterol da suka hada da tramadol da aspirin zuwa viagra da dai sauransu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here