Majalisar Dattawa ta ƙasa ta tabbatar da Sanata Jimoh Ibrahim na APC daga Ondo ta Kudu, tsohon shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa mai zaman kanta, Farfesa Mahmoud Yakubu, Sanata Ita Enang, Reno Omokri, Sanata Grace Bent da Sanata Farfesa Nora Ladi Daduut a matsayin waɗanda aka naɗa jakadu ba na aikin ƙwararru ba.
Haka kuma, a ranar Alhamis, majalisar ta tantance tare da amincewa da Ibok-Ete Ekwe Ibas, tsohon babban jami’in kula da jihar Rivers kuma tsohon shugaban rundunar sojan ruwa daga jihar Cross River, a matsayin jakada ba na aikin ƙwararru ba, da Chioma Ohakim, tsohuwar uwargidan gwamnan jihar Imo, da Abdulrahman Dambazau, tsohon ministan harkokin cikin gida kuma tsohon shugaban rundunar sojan ƙasa, da tsohon ministan lafiya Femi Fani Kayode, da Erelu Angela Adebayo daga Ekiti, da Florence Ajimobi daga Oyo, da Chioma Ohakim.
Jerin ya ƙunshi jakadu da manyan kwamishinoni 34 na aikin ƙwararru, da jakadu da manyan kwamishinoni 30 ba na aikin ƙwararru ba, inda adadin duka ya kai mutum 64.
Tabbatarwar ta biyo bayan gabatarwa da nazarin rahoton kwamitin kula da harkokin waje na majalisar dattawa, wanda shugabansa Sanata Sani Bello na APC daga Niger ta Arewa ya gabatar. Rahoton ya bayyana cewa an kammala duba dukkan waɗanda aka naɗa tare da tabbatar da cancantarsu.
Daga cikin fitattun sunayen jakadun aikin ƙwararru 34 akwai Sulu-Gambari Olatunji Ahmed daga jihar Kwara, Segun Ige daga jihar Edo, da Odumah Yvonne Ehinosen daga jihar Edo.
A yayin gabatar da rahoton, Sanata Bello ya bayyana cewa an ga dukkan waɗanda aka naɗa sun cancanta, kuma babu wani ƙorafi ko ƙara da aka shigar a kansu game da naɗin nasu.
Bayan tabbatarwar, shugaban majalisar dattawa Sanata Godswill Akpabio ya taya su murna, tare da ƙarfafa musu gwiwar wakiltar Nijeriya yadda ya kamata a ƙasashen da za su yi aiki.
Haka kuma, ya roƙi Sanata Jimoh Ibrahim da ya ci gaba da hulɗa da majalisar dattawa domin ta ci gaba da amfana da ilimi da gogewarsa.













































