Hukumar gudanarwa ta Kwalejin aikin Noma ta Audu Bako dake Dambatta ta musanta zargin cewa ta ki bin umarnin gwamnatin jihar Kano.
Shugaban kwalejin, Farfesa Muhammad Audu Wailare, ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a ranar Litinin.
Ya ce zargin ya samo asali ne daga batun dakatar da wani malami, Malam Ahmad, wanda ake tuhuma da dukan abokin aikinsa a bainar jama’a.
Farfesa Wailare ya bayyana cewa matakin ladabtarwar an dauke shi ne tare da hadin gwiwar hukumar ma’aikata ta jihar Kano, ba wai kwalejin kadai ta dauki matakin ba kamar yadda wasu rahotanni suka yi ikirari.
Ya zargi shugaban kungiyar malamai ta ASUP a Arewa maso Yamma, Dakta Abdulaziz Badaru, da kokarin bata suna ta hanyar yada bayanan da ba su da tushe.
Sai dai a baya kungiyar ASUP ta Arewa maso Yamma ta zargi kwalejin da kin bin umarnin gwamnati na mayar da shugabanta a kwalejin, Malam Ahmad Haruna Muhammad, wanda aka cire daga mukaminsa.
Kungiyar ta bayyana cewa binciken da gwamnati ta gudanar ya wanke shi, sannan aka nuna cewa ba a bi ka’ida wajen dakatar da shi ba.
ASUP ta jaddada cewa tana da kyakkyawar alaka da gwamnatin jihar Kano, musamman wajen kula da walwalar malamai da inganta kayan koyarwa.
Duk da haka, ta sha alwashin ci gaba da matsa lamba domin tabbatar da bin umarnin gwamnati tare da sake kiran kwalejin da ta dawo da Malam Ahmad bisa umarnin hukumomi.













































