Kotu a birnin Lagos ta yanke wa mutane biyar hukuncin zaman gidan yari kan laifin safarar miyagun ƙwayoyi da aka kama su da su a filin jirgin sama na Murtala Muhammad dake Ikeja, bayan binciken hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta kasa ya tabbatar da laifinsu.
Binciken hukumar ya gano cewa wasu daga cikin su, Olasupo Michael Oladimeji, Muaezee Ademola Ogunbiyi da Sola Adegoke, an kama su da Cocain mai nauyin kilo goma sha bakwai da digo tara da suka ɓoye a cikin kaya da tsafe-tsafen gargajiya da za a tura zuwa birnin Sydney na ƙasar Australia.
Hukumar ta ci gaba da bincike inda ta gano ƙarin kwaya iri canadian loud mai nauyin kilo ashirin da digo biyar a gidan Ogunbiyi da ke Lekki, da kuma kwace motar range rover mai launin baƙi daga gidan Adegoke a unguwar Ikeja gra domin tabbatar da shaidu.
An gurfanar da mutanen ukun a gaban mai shari’a Musa Kakaki na babbar kotun tarayya da ke Lagos, inda suka amsa laifukan da ake tuhumar su da su sannan kotun ta yanke musu hukuncin zaman gidan yari na shekaru biyar ga kowane ɗaya tare da ƙwace motocin da aka samu tare da su domin mika su ga gwamnatin tarayya.
A wata shari’ar daban, hukumar ta kama wasu shugabannin ƙungiyar safarar miyagun ƙwayoyi biyu, Obunike Obichukwu da Uzorchukwu Chukwurah, bayan gano Cocain kilo biyu da digo sittin da tramadol kilo ashirin da digo tara da suka ɓoye a cikin kayan motoci da za a tura ƙasar Gabon.
Bayan amsa laifi, kotu ta yanke musu hukuncin zaman gidan yari na shekaru uku ko biyan tara naira miliyan biyu ga kowane ɗaya tare da ƙwace naira miliyan huɗu daga ɗaya daga cikinsu ya bayar domin cin hanci ga jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta kasa.
Hukumar ta bayyana cewa waɗannan hukunci sun nuna sabuwar dabarar ta na bin diddigin manyan jagororin ƙungiyoyin miyagun ƙwayoyi da dukiyoyin da suke samu ta hanyar laifi domin kare al’umma daga aikata safarar miyagun ƙwayoyi a filayen jiragen sama na Najeriya.













































