Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta kama wani gawurtaccen wanda ake zargi da aikata fashi da makami, mai suna Abba Aliyu da aka fi sani da Abba Fiya, biyo bayan gaggawar amsa kiran neman taimako da aka samu a rukunin gidajen unguwar Hausawa a cikin birnin Kano.
Wannan bayani ya fito ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a ranar Litinin.
Sanarwar ta bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne a ranar Lahadi, 21 ga Disamba, 2025, ta hannun jami’an sashen Anti-Daba na rundunar ƴan sandan, yayin da suke amsa rahoton wani lamari na fashi da makami.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa wanda ake zargin, mai shekaru 26 da ke zaune a unguwar Dala a Kano, an san shi da ƙwarewa wajen aikata fashi da makami, kuma an ƙwato wuka mai kaifi a hannunsa a lokacin kamen.
Sanarwar ta ƙara da cewa a yayin bincike, Abba Fiya ya amsa cewa yana da hannu a cikin wasu fashi da makami da dama da kuma rikice-rikicen ƙungiyoyin daba a yankuna kamar Gobirawa Gangare, Dala da Tudun Fulani Mayanka a jihar Kano, tare da amincewa da aikata laifuka da suka janyo mutuwa, raunuka da sace dukiya a jihohin Kano, Rivers da Lagos.
Rundunar ƴan sandan ta bayyana cewa bincike kan lamarin na ci gaba da gudana, tare da tabbatar da cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala binciken.
Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin, tare da ƙarfafa gwiwar jama’a da su ci gaba da ba da haɗin kai ga hukumomin tsaro ta hanyar kai rahoton duk wani motsi ko aiki da ake zargi, tare da tuntuɓar ofishin ƴan sanda mafi kusa ko layukan gaggawa na rundunar.













































