Gwamnatin tarayya ta kashe sama da Naira Biliyan 150 wajen tallafa wa ɗalibai 788,000 a ƙarƙashin shirin Asusun bada Lamunin Ilimi na Najeriya, wanda aka fi sani da NELFUND, domin bunƙasa ilimi da rage wa iyaye nauyin kuɗin karatu.
Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na ƙasa, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana hakan ne a taron manema labarai na ƙarshen shekara da aka gudanar a birnin Abuja, inda ya yi bayani kan ayyukan da gwamnati ta aiwatar a sassa daban-daban.
Ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta samu manyan nasarori a fannoni da dama, musamman a ɓangaren ilimi, inda aka fi mayar da hankali kan matasa da bunƙasa basirarsu ta hanyar tsare-tsare masu tasiri.
Ministan ya ƙara da cewa shekarar 2025 ta kasance shekara mai cike da manufofi da aiwatar da tsare-tsare masu tasiri, musamman waɗanda ke da nufin tallafa wa matasan Najeriya ta hanyar ilimi da bunƙasa ƙwarewa.
Ya bayyana cewa shirin Asusun Lamunin Ilimi na Najeriya ya tallafa wa sama da ɗalibai 788,000 da lamuni marar ruwa da tallafin kuɗi da ya haura Naira Biliyan 150, kuma shirin na ci gaba da faɗaɗa domin kai wa ƙarin ɗalibai ɗauki.
Haka kuma, gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da shirin zuba jari a harkokin fasahar zamani da ƙirƙire-ƙirƙire, wanda aka sani da Zuba Jari a Harkokin fasahar zamani da Ƙirƙire-ƙirƙire.
An kuma ƙaddamar da tallafin jarin kasuwanci ga ɗalibai masu ƙirƙira a fannonin kimiyya, fasaha, injiniya, lissafi da likitanci, inda ake ba su kuɗin da ba sai an mayar ba har zuwa Naira Miliyan 50, tare da shirin Ƙwararrun Fasaha Miliyan Uku da ke gina babbar rundunar ƙwarewar fasahar zamani a Afirka.
NAN













































