Jibril ne daga Sudan’ Cin fuska ne ba abin dariya ba – Buhari

Muhammadu Buhari 1
Muhammadu Buhari 1

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ikirarin cewa shi Jubril ne daga kasar Sudan hadin bakin wasu ‘yan Najeriya ne dake son kawar da hankalin gwamnatinsa daga manyan batutuwa.

Buhari ya bayyana haka ne a cikin wani shirin faifan bidiyo mai suna ‘Bikin Dan Kishin Kasa, Jagora’, wanda aka nuna yayin liyafar cin abinci na sirri a Abuja domin murnar cikarsa shekaru 80 a duniya.

Shugaban na mayar da martani ne kan wani makirci da aka fara kullawa tun a shekarar 2018 cewa ya mutu kuma wani Jubril dan kasar Sudan ne a matsayin sa.

Wannan jita-jita ta yadu ne a lokacin da Buhari ya dawo daga kasar Ingila bayan ya shafe wasu watanni yana jinyar wata cuta.

A cikin shirin, Buhari ya danganta wannan jita-jita da ayyukan bata-gari wadanda a cewarsa kawai suna cin fuska ne.

Da aka tambaye shi ko me zai sashi jimami idan ya bar mulki a 2023, Buhari ya ce ba zai yi kewa da yawa ba, yana mai cewa wasu mutane da ke ganin za su iya tsoratar da shi ne ke cin zarafinsa. Ya kuma ce yana iya bakin kokarin sa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here