Hukumar Kula da Gyaran Hali ta Ƙasa (NCoS) ta hana wani yunƙuri na shigar da abubuwan da ake zargin miyagun ƙwayoyi masu shafar kwakwalwa cikin gidan gyara na tsaka-tsaki da ke Kuje, Babban Birnin Tarayya Abuja.
Mai magana da yawun hukumar a Abuja, Mista Samson Duza, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
Ya ce da misalin ƙarfe 12:45 na rana a ranar Asabar, wani mutum mai suna Njimogu Ikedi ya zo ziyarar ɗan gidan, inda aka same shi da abubuwan da ake zargin tabar wiwi da wasu ƙwayoyi masu sa maye, da ya ɓoye a cikin kayansa.
Duza ya ce jami’an tsaro da ke bakin aiki ne suka gano kayan da aka ɓoye yayin binciken tsaro na yau da kullum.
Karin labari: Fursunoni 68 a Kano sun yi nasara a jarabawar NECO ta 2025
Ya ƙara da cewa Kwamandan hukumar a Abuja, Mista Christopher Jen, ya bayar da umarnin kama mutumin tare da mika shi ga Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) domin ci gaba da bincike da gurfanarwa.
Jen ya gargadi masu kawo ziyara da ke da mugun nufi da su daina irin wannan aiki, yana mai tabbatar da cewa jami’an hukumar za su ci gaba da tona duk wata dabara ta shigar da kayan da aka haramta.
Ya kuma roƙi al’umma da ‘yan Najeriya masu kishin ƙasa da su ci gaba da goyon bayan hukumar wajen gyara da sake tarbiyyar masu laifi, domin samar da tsaro da zaman lafiya a cikin al’umma.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa wannan lamari ya biyo bayan irin wannan kama a watan Yuli 2024, lokacin da aka cafke wata mata da ta yi ƙoƙarin shigar da miyagun ƙwayoyi cikin wannan gidan gyara.













































