Hukumar kula da gidajen ajiya da gyaran hali ta Najeriya, shiyyar Kano, ta bayyana cewa fursunoni 68 sun yi nasara a jarabawar (NECO) ta shekarar 2025.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, CSC Musbahu Lawan Kofar Nassarawa, ya fitar a ranar Litinin.
Sanarwar ta ce nasarar ta samu ne karkashin shirin Cibiyar Ci gaba da Ilimi ga Fursunoni, tare da tallafin gwamnatin jihar Kano wadda ta dauki nauyin daliban.
Sanarwar ta kara da cewa wannan shiri ya yi daidai da dokar Gyaran Hali ta 2019, wadda ta mayar da hankali kan farfado da fursunoni ta hanyar ilimi da sana’o’in koyarwa.
Haka kuma, ya yi daidai da umarnin Babban Kwamandan hukumar na kasa, Selvester Indidi Nwakuche, wanda ya umurci shugabannin cibiyoyin gyaran hali a fadin kasar da su rika saka fursunoni a shirye-shiryen ilimi da na sana’a.
Rahoton ya ce hukumar ta kara bayyana cewa gwamnatin Kano ta sake nanata kudirinta na inganta rayuwar fursunoni ta hanyar samar musu da damar ilimi domin su iya sake komawa cikin al’umma bayan kammala zaman gidan yari.
Shugabar kwamitin bayar da afuwa, Hajiya Azumi Namadi Bebeje, ta taya fursunonin murnar nasarar, tare da gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa goyon bayansa.
Haka zalika, Kwamandan Gyaran Hali na Kano, Ado Inuwa, ya bayyana farin cikinsa kan wannan nasara, inda ya yi musu fatan ci gaba da samun nasara a tafarkin gyaran hali da kuma komawa cikin al’umma a matsayin nagari.












































