Hatsarin mota ya hallaka ƴan sanda uku a Kaduna

342873172 902673187480662 5566809744289880446 n
342873172 902673187480662 5566809744289880446 n

Wasu ‘yan sanda uku sun rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a garin Kidanda da ke karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna.

Ƴan sandan na tafiya ne zuwa karamar hukumar Giwa bayan halartar bikin Hawan Dauche a birnin Zariya a ranar Lahadi, inda hatsarin ya afku da misalin karfe 9 na dare.

An ruwaito cewa ɗaya daga cikin tayoyin motar ‘yan sanda ne ya fashe a kauyen Sako, a Kidanda, wanda kuma ya yi sanadiyar mutuwar jami’an guda uku.

Wasu uku kuma sun jikkata, inda aka garzaya da su asibiti domin kula da lafiyarsu a cewar majiyoyi.

Hotuna da aka gani, sun nuna jami’an jina-jina, inda wasu suka samu munanan raunuka a kawunansu.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Mohammed Jalige, ya tabbatar da faruwar hatsarin tare da yi wa jami’an da suka rasu addu’a da kuma fatan samun sauki ga waɗanda suka jikkata.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here