Shugaba Bola Tinubu zai kafa wani kwamiti mai karfi da zai binciki yadda fashe-fashen motocin dakon man fetur ke faruwa da kuma aiwatar da matakan kare kai domin dakile afkuwar lamarin.
Ministan yada labarai, Mohammed Idris ne ya bayyana haka a ranar Lahadi a fadar Sarkin Suleja, inda ya kai ziyara domin jajantawa wadanda fashewar tanka ta afku a ranar Asabar a mahadar Dikko, a karamar hukumar Gurara ta Jihar Neja.
Idris ya ce za a fitar da mambobin kwamitin ne daga ma’aikatar yada labarai da wayar da kan jama’a, ma’aikatar jin kai, kungiyar dillalan man fetur ta Najeriya IPMAN, kungiyoyin direbobin tanka da sauran masu ruwa da tsaki.













































