Gwamnatin tarayya ta amunce da kara alawus-alawus din ma’aikatan lafiya wadan da ba’a asibiti suke aiki ba.
Hakan na dauke a cikin wata sanarwa da shugan hukumar dake kula da biyan albashi ta kasa, Ekpo Nta, mai dauke da kwanan watan 26 ga watan Yuli na shekarar 2023 ya fitar.
Sanarwar ta nuna cewa alawus din ma’aikatan lafiyan dake kan matakin aiki na 1 zuwa na biyar, an mayar musu dashi 10,000 wanda da dubu 5,000 ake basu.
Haka kuma ma’aikatan dake kan mataki na 6 zuwa na 15 an mayar dashi N18,000 a maimakon N10,000.












































