Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun 25-26 ga watan Disamba, da 1 ga watan Junairu, 2025, a matsayin ranakun hutu.
Bukukuwan Kirsimeti, Ranar Dambe da na Sabuwar Shekara.
Olubunmi Tunji-Ojo, ministan harkokin cikin gida ne ya sanar da ranakun a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babbar sakatariyar ma’aikatar Magdalene Ajani.
Ya taya ‘yan Najeriya murnar hutu tare da bukace su da su yi amfani da lokacin bukukuwan wajen yin tunani kan kimar soyayya, zaman lafiya da hadin kai ga Najeriya.













































