Gwamnatin tarayya da ta jihar Katsina sun sake fasalin tsarin rage mace-macen mata masu juna biyu da jarirai

L R Governor Umar Radda and Prof. Ali Pate

Gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar Katsina suka kaddamar da shirin rage mace-macen mata masu juna biyu (MAMII) a matsayin dabarun rage mace-macen mata da jarirai a kasar nan.

Dakta Muntaqa Sadiq-Umar, babban jami’in ofishin hadin gwiwa na sassan na kasa, ya bayyana hakan a Katsina, inda ya ce an dauki wannan shiri ne da nufin magance matsalar rashin lafiya da ke da nasaba da mace-macen mata da jarirai.

Mista Omorugi Iyahen ne ya wakilci jami’in.

A cewar Sadiq-Umar shirin MAMII ta hada dukkan masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya domin samar da hanyoyin magance yawan kididdigar da qke samu nq mace-macen mata da jarirai.

Ya bayyana cewa kananan hukumomi 172 a fadin Najeriya sun fuskanci yawaitar mace-macen mata masu juna biyu da jarirai, inda 15 daga cikinsu ke jihar Katsina.

Karin karatu: Zazzabin Lassa: Sama da ma’aikatan AKTH 20 da aka gwada basa ɗauke da cutar 

A nata jawabin, uwargidan gwamnan jihar Katsina, Hajiya Zulaihat Dikko Radda, ta yabawa gwamnatin tarayya bisa wannan shiri, inda ta ce hakan zai taimaka matuka wajen ceto rayuwar mata da yara.

Dikko-Radda ta kara da cewa kungiyar tata ta dauki masu aikin sa kai guda 50 a halin yanzu suna aiki a cikin al’umma don zaburar da mata da kuma tabbatar da cewa sun samu kulawar haihuwa a cibiyoyin lafiya.

Shi ma da yake jawabi, babban jami’in kungiyar MAMII na jihar, Dr Aminu Lawal, ya bayyana cewa jihar Katsina na daya daga cikin jihohin da ke fama da mace-macen mata masu juna biyu da jarirai.

Ya danganta yawan mace-macen da ake samu da jinkiri daban-daban, da suka hada da jinkirin neman lafiya da kuma jinkirin isa ga cibiyoyin kiwon lafiya.

Sauran jinkirin sun haɗa da na samun isasshen kulawa, ɗaukar nauyi, da jinkiri wajen daidaita ayyuka.

Dr Shamsuddeen Yahaya shi ne babban sakataren hukumar kula da lafiya matakin farko na jihar, ya bayyana cewa kananan hukumomin Katsina, Kaita, Daura, Mani, da Batagarawa ne aka fi samun yawan mace-macen mata masu juna biyu a jihar.

Ya bayyana sakamakon binciken da aka gudanar tsakanin watan Disamba 2023 zuwa Nuwamba 2024, inda ya danganta mafi yawan wadannan mace-mace da zubar jini na haihuwa da kuma ciwon hawan jini na ciki, da dai sauransu.(NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here