Gwamnatin Kano ta fara biyan kudin diya na aikin hanyar Kabuga, Rimin Gado, Gwarzo Zuwa Dayi 

Abba Kabir Yusuf Kano Kano 715x430

Gwamnatin jihar Kano fara biyan diyar aikin titin gwamnatin tarayya, Wanda ya taso tun daga Kabuga, Rimin Gado, Gwarzo zuwa Dayi.

Da yake jawabi ga al’ummar wadan nan yankuna, Kwamishinan Kula da ayyuka na musamman Alh. Nasiru Sule Garo, yace biyan kudade da gwamna ya sahale a biya ya nuna karara irin jajircewarsa da Kuma tausayawa al’umma a duk Sanda Wani abu ya gifta wanda ya ke bukatar daukin gaggawa.

Haka Kuma Kwamishinan ya Kara da cewa an samar da wannan jimillar Kudin ne Sama da naira biliyan biyu ga al’umomin wadan nan kananan hukumomin da suka hada da Ungogo, Tofa da Rimin Gado da Kabo harma da karamar hukumar Gwarzo domin tallafa musu sakamakon wannan aikin hanya da yabi ta kan kadarorinsu.

Wannan biyan diyya ana sa ran zai kawo karshen tafiyar hawayniya da aikin yakeyi musamman don kaucewa hadurra da suke faruwa yanzu haka akan hanyar da kuma wahalhalun da masu amfani da hanyar da kuma mutanen garuruwan da suke kan hanyar suke ciki.

Kwamishinan ya kara da cewa tuni gwamnatin Alh. Abba Kabir Yusuf ta amince da fara biyan wannan kudi ba tare da Wani bata lokaci ba, ga jama’ar da wannan aiki ya shafa Kamar yadda aka tsara.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here