Gwamnati na shiri kwaso ƴan Najeriya daga Isra’ila da Iran

Evacuation

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da kammala shirinta na kwashe ‘yan Najeriyar da suka makale a kasashen Isra’ila da Iran, biyo bnayan tashin hankalin da ya barke tsakanin kasashen biyu.

A wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Kimiebi Ebienfa ya fitar a daren jiya Talata, ma’aikatar ta tabbatar da cewa ofisoshin jakadancin Najeriya a Tel Aviv da Tehran na ci gaba da kai dauki ga ‘yan kasar nan da rikicin ya shafa kuma suna kokarin ganin an kwashe su cikin koshin lafiya.

Ma’aikatar ta bukaci ‘yan Najeriya mazauna kasashen biyu da su bi ka’idojin tsaro da kuma gaggauta tuntubar ofishin Jakadancin Najeriya ko Ofishin Jakadancin mafi kusa don yin rajista da kuma yi musu jagoranci.

Ma’aikatar ta yaba da jajircewar ofisoshin jakadancin Najeriya a Isra’ila da Iran tare da jaddada kudurin gwamnati na kare ‘yan Najeriya da ke kasashen waje.

Sanarwar ta kara da cewa, za a sanar da karin bayani kan yadda za a kwashe mutanen ta hanyar shafukan sadarwa na na gwamnati.

Matakin na gaggawa ya biyo bayan hare-haren wuce gona da iri da Isra’ila ta kai ranar Juma’a, wanda ya kai kusan wurare 100 a duk fadin kasar Iran, ciki har da makaman nukiliya da na soji.

Rahotanni sun ce hare-haren sun kashe wasu manyan hafsoshin sojin Iran.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here