Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa gwamnatinsa tana da cikakken shiri da kuduri wajen tabbatar da jin dadin ’yan jarida da samar da ingantaccen yanayin aiki a fadin jihar.
Gwamnan ya bayyana wannan ne a ranar Lahadi yayin jawabi a wajen taron horaswa na kwanaki biyu da gwamnatin Kano ta shirya wa Kungiyar masu aiki da rahotanni ta Kano, wanda aka gudanar a Jihar Kaduna.
A wata sanarwa da Usman Gwadabe, Daraktan Wayar da Kai na Fadar Gwamnati ta Kano, ya fitar a ranar Litinin, ta bayyana cewa gwamnan ya tabbatar da ci gaba da gina dangantaka mai kyau tsakanin gwamnati da kafafen yada labarai domin inganta hidimar jama’a.
Gwamnan, wanda Sakataren Gwamnatin Jihar Kano Umar Farooq Ibrahim ya wakilta, ya bukaci samun hadin kai na gaskiya tsakanin gwamnati da ’yan jarida maimakon yin gogayya a wajen hidimar al’umma, tare da kira ga ’yan jarida su kiyaye ka’idojin aikinsu yayin da gwamnatin ke tabbatar da bude hanyoyin isar da bayanai ga jama’a.
Ya gode wa masu aiki da rahotanni bisa jajircewarsu wajen tallafa wa gwamnati ta cimma manufofinta, tare da nuna godiya ga Gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani bisa damuwarsa kan batutuwan tsaro da ke addabar wasu yankunan arewacin kasar, sannan ya tabbatar da cewa Kano za ta ci gaba da daukar matakai na ingantaccen tsaro.
A nasa bangaren, wakilin Gwamnan Kaduna, Kwamishinan Yada Labarai Ahmed Maiyaki, ya yaba wa gwamnatin Kano bisa shirya taron a Kaduna, yana mai bada shawarar ci gaba da aiki tare domin tabbatar da rikon amana da samar da ingantaccen mulki ga jama’a.
Da yake jawabi Kwamishinan Yada Labaran Kano Ibrahim Abdullahi Waiya ya bayyana cewa an dauki nauyin taron ne domin kara ilimi da karfafa zumunci tsakanin gwamnati da ’yan jarida.
Ana nasa jawabin Daraktan yaɗa Labaran Gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya bukaci ’yan jarida su ci gaba da mutunta zaman lafiya da jihar ke samu tun zuwan Gwamna Yusuf.
Shugaban Kungiyar Marubuta Labarai Murtala Adewale ya nuna godiya ga gwamnatin jihar bisa shirya taron a wajen Kano, yana mai cewa wannan shi ne irinsa na farko tun kafuwar kungiyar.
Taron ya kunshi tattaunawa tsakanin ’yan jarida da jami’an gwamnati, bayar da takardun shaida, tare da gabatar da takardu guda biyar da masana suka shirya.
Farfesa Sule Yau Sule ya gabatar da muƙala mai taken “KarfafaDangantaka Tsakanin ’Yan Jarida Da Gwamnati: Muhimmancin Kula Da Ka’idojin Aiki.”
Sauran muƙalun sun hada da “Matsin Lamba Da Kammala Aiki: Hanyoyin Kare Lafiyar Ƙwaƙwalwa” wadda Dr. Aminu Ibrahim Shehu ya gabatar; sai “kiyaye Kalaman Batanci A Kafafen Yada Labarai: Ta Fuskar Doka” wadda Barrister Yusuf Abdulsalam ya gabatar; “Amfanin fasahar AI A Aikin Jarida Da Yada Labarai: matsaloli Da Amfani” tare sa Hajiya Sani; da “kafofin yaɗa labarai na zamani: Sabbin Damarmaki Da Kalubale” tare da Abdullateef Abubakar Jos.












































