Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya amince da murabus din Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Umar Haruna Doguwa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu ranar Talata.
Hon. Umar Haruna Doguwa ya mika takardar murabus dinsa a hukumance ranar Litinin, 2 ga Maris, 2026, wanda zai fara aiki daga yau.
SolaceBase ta rawaito cewa murabus dinsa na iya kasancewa yana da alaka da takarar shugabancin Jam’iyyar (APC) ta Jihar Kano, inda ake cewa ana hasashen Doguwa na daga cikin masu neman takarar a taron jam’iyyar na jiha da aka shirya yi a yammacin Talata a filin wasa na Sani Abacha.
Gwamna Yusuf ya bayyana matukar godiyarsa ga Hon. Doguwa bisa jajircewarsa, biyayyarsa da kuma sadaukarwar da ya yi wa al’umma da gwamnatin Jihar Kano.
Gwamnan ya tuna cewa Hon. Doguwa ya taba rike mukamin Kwamishinan Ilimi, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa manufofi da gyare-gyaren ilimi, ciki har da ayyana dokar ta-baci a bangaren ilimi, kafin daga bisani a mayar da shi Ma’aikatar Albarkatun Ruwa.
Ya kara da cewa cikin shekara guda da ya jagoranci Ma’aikatar Albarkatun Ruwa, an samu gagarumin cigaba wajen gyaran cibiyoyin samar da ruwa da kuma fadada samar da tsaftataccen ruwan sha ga al’ummomi da dama a fadin jihar.
Gwamna Yusuf ya kuma ce jagorancin Hon. Doguwa ya taimaka wajen karfafa kwarewar ma’aikata a ma’aikatar tare da inganta ayyukan hidima daidai da manufar gwamnati na samar da dorewar samun ruwa ga dukkan ‘yan kasa.
Gwamnan ya bayyana Hon. Doguwa a matsayin ma’aikacin gwamnati mai da’a da kwazo, wanda gudummawarsa za ta ci gaba da kasancewa cikin nasarorin da gwamnatin ta samu.
Ya yi masa fatan alheri a kokarinsa na gaba, tare da tabbatar masa cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da gina kan nasarorin da aka samu a bangaren Albarkatun Ruwa.
Gwamna Yusuf ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na tabbatar da samar da ruwa ba tare da tangarda ba da kuma inganta jin dadin al’ummar Jihar Kano.
Daga bisani, gwamnan ya umarci Kwamishinan Ma’aikatar Ilimi, Gwani Dr Ali Haruna Abubakar Makoda, da ya rike ragamar Ma’aikatar Albarkatun Ruwa har sai an nada ko a sauya sabon Kwamishina a hukumance.













































