Fadar shugaban ƙasa ta musanta rahotannin da ke cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu zai ziyarci ƙasar Amurka a ranar Talata domin ganawa da mataimakin shugaban ƙasar, J.D. Vance.
Mai taimaka wa shugaban ƙasa na musamman kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Temitope Ajayi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Litinin.
Ajayi ya bayyana rahoton a matsayin karya da ruɗani, inda ya ce babu wani shiri na irin wannan tafiya da ake yayatawa.
Ya ƙara da cewa idan har shugaban ƙasa Tinubu zai kai ziyara fadar White House, zai gana kai tsaye da shugaban ƙasar Amurka Donald Trump, ba tare da shiga tattaunawa da mataimakin shugaban ƙasa ba.
Fadar shugaban ƙasa ta kuma tunatar da cewa tun da farko mai ba da shawara na musamman ga shugaban ƙasa kan yaɗa manufofi, Daniel Bwala, ya bayyana cewa Tinubu da Trump suna da haɗin gwiwa a yaƙi da ta’addanci da yaki da ayyukan tayar da kayar baya, kuma ana iya samun ganawarsu a nan Abuja ko kuma Washington D.C. nan gaba kaɗan.
Haka zalika, sanarwar ta nuna cewa tattaunawar shugabannin biyu za ta mai da hankali ne kan yadda za a ƙarfafa haɗin kai wajen yaki da ta’addanci da kare ‘yancin bil’adama, tare da magance bambance-bambancen ra’ayoyi game da hare-haren masu ta’addanci da ke faruwa a Najeriya.












































