A ranar Alhamis, 17 ga watan Agusta, Hedkwatar tsaro, ta bayyana cewa jami’an sojoji 36 aka kashe a jihar Neja. Darektan watsa labarai na hukumar tsaron, Manjo Janar Edward Buba, ne ya bayyana hakan yayin da yake bayyana adadin mutanen da aka kashe a harin kautan baunar da aka kaiwa sojoji a jihar ta arewa maso gabas a ranar Litinin, 14 ga watan Agusta.
Da aka tambaye shi game da ainahin abun da ya haddasa hatsarin jirgin, ya bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike don gano musababbin abun sannan ya bukaci jama’a da su yi hattara da farfagandar ‘yan ta’adda, sannan su ci gaba da zama masu kishin kasa.
Ya kuma sha alwashin cewa babu kungiyar da za ta iya farmakar dakarun sojojinta sannan ta ci bulus. Buba ya ce: “Babu kungiyar da za ta farmaki dakarunmu ba tare da ta wani mummunan sakamako ba.”
Yan ta’adda sun yi wa dakarun sojoji kautan bauna a yankin Zungeru da ke jihar, kuma wasu dakarun sojin Najeriya da dama sun kwanta dama a harin. Hakazalika, jirgin sojojin sama mai lamba MI-171 da ya je aikin kwashe wanda aka kashen ya yi hatsari a ranar Litinin a karamar hukumar Shiroro da ke jihar.
Sojoji 13 ne aka kashe a ranar Lahadi, yayinda kuma aka kashe 8, cikinsu har da Kyaftin ɗaya da kuma Manjo ɗaya a harin kwanton ɓaunar da ya wakana ranar Litinin. Rahoton ya bayyana cewa sojojin sun yi yunkurin tare ‘yan ta’addan ne da aka ce sun sato shanu masu tarin yawa a wani ƙauye mai suna Kundu.