Jami’an Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) sun kai sumame gidan tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello a Abuja.
Kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana, jami’an EFCC sun yi wa gidan tsohon gwamnan kawanya tun karfe 9 na safiyar Laraba.
A baya dai EFCC ta gurfanar da Yahaya Bello, da dan uwansa Ali, Dauda Sulaiman, da kuma Abdulsalam Hudu a gaban mai shari’a James Omotosho na babbar kotun tarayya da ke Abuja, a kan tuhumar da aka yi masa a watan Maris 2024 kan zargin karkatar da kudi N84bn.