Ministan tsaro na ƙasa Alhaji Mohammed Badaru Abubakar ya yi murabus daga mukaminsa nan take bisa dalilan rashin lafiya.
A cikin wasiƙar da ya tura wa shugaban ƙasa Bola Tinubu mai ɗauke da ranar 1 ga Disamba, ya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne domin kulawa da lafiyarsa.
Shugaban ƙasa Tinubu ya amince da murabus ɗin nasa tare da gode masa bisa hidimar da ya bayar ga ƙasa tun lokacin da aka naɗa shi.
Ana sa ran shugaban ƙasa zai sanar da majalisar Dattawa wanda zai maye gurbin Badaru a makon nan idan shirye-shirye sun kammala.
Badaru Abubakar mai shekaru sittin da uku ya kasance tsohon gwamnan jihar Jigawa na wa’adin shekaru takwas daga 2015 zuwa 2023, kafin a naɗa shi minista a ranar 21 ga watan Agusta 2023.
Murabus ɗinsa ya zo a daidai lokacin da shugaban ƙasa ya ayyana dokar ta baci kan tsaro tare da shirin bayyana tsarin aiwatar da wannan mataki a nan gaba.













































