Shugaban Hukumar Yaki da masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya ce hukumar ta sanya ido kan wasu gwamnonin jihohi uku da ke kan karagar mulki bisa yunkurinsu na karkatar da biliyoyin Naira ta hanyar kokarin biyan ma’aikata albashinsu a hannu.
Bawa, ya ce za a ci gaba da kai samame kan ma’aikatan ofishin ‘Bureau De Change’, inda ya bukaci ‘yan Najeriya da su tallafa wa tsarin, domin amfanin kowa.
Tun a ranar 26 ga watan Oktobar 2022 ne Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa za a sake fasalin kudin kasar don magance matsaloli da dama da ke da illa ga tattalin arzikin kasar.
Yayin da za a fitar da takardun da aka sakewa zayyana a ranar 15 ga watan Disambar Shekarar nan ta 2022.
Kazalika al’ummar Najeriya suna da damar ci gaba da kaiwa tsafaffin kudin ga gabankuna har zuwa ranar 31 ga watan Janairun Shekarar 2023.
To sai dai kuma Wani Abu da manyan ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa da masu saka hannun jari da sauran jama’a ke yi na yin kaca-kaca da karkatar da kudaden da aka boye zuwa dala, kadarori da sauransu, ya haifar da tada jijiyar wuya.
Gwamnan babban bankin kasa CBN, Godwin Emefiele, ya ce an dauki matakin ne domin yaki da ayyukan ta’addanci da kuma tara kudaden jama’a.
Babban bankin zai sake fasalin takardun kudi na Naira 200 da Naira 500 da Naira 1,000.
Rahotanni sun bayyana cewa ko a ranar Alhamis 3 ga watan Nuwambar nan na 2022 a kasuwannin bayan Fagge dake Abuja ana sayar da dala kan Naira 882, duk da samame da jami’an EFCC suka kai a jihohin Legas da Kano da Kuma Birnin Tarayya Abuja.










































