Bamu da shirin sauya sunan babbar hanyar Murtala Mohammed-Gwamnati

Wole Soyinka 1
Wole soyinka

Halima Lukman

Gwamnatin tarayya ta yi watsi da rahoton da ke cewa an sauya wa babbar hanyar Murtala Mohammed da ke babban birnin tarayya Abuja suna Wole Soyinka.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, mataimaki na musamman kan harkokin watsa labarai ga ministan yada labarai da wayar da kan Jama’a Rabiu Ibrahim, ya ce gwamnatin Tarayya ba ta sauya wa babbar hanyar suna ba kuma ba ta shirin hakan.

Karanta kari: Gwamnatin tarayya ta ayyana Laraba a matsayin hutun tunawa da Dimokuradiyyar bana

Sanarwar ta kara da cewa, wannan gwamnatin karkashin jagorancin Bola Tinubu, ba ta taba tunanin sauya sunan babbar hanyar Murtala Mohammed da ke birnin tarayya ba.

Yace, “Idan ba a manta ba, a ranar 4 ga watan Yunin 2024, shugaban kasa Bola Tinubu ya kaddamar da wata sabuwar hanya a babban birnin tarayya Abuja da ake kira Arterial Road N20 da ta tashi daga Katampe zuwa Jahi, ta kuma dangana da babban titin Murtala Mohammed zuwa babbar hanyar Ahmadu Bello”.

“Yayin kaddamar da sabuwar hanyar da aka yi wa lakabi da Arterial Road N20, Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya bai wa shugaban kasa shawarar a sanya wa hanyar sunan Farfesa Wole Soyinka, kuma shugaban ya amince,” in ji Gwamnatin Tarayya.

Karanta kari:Yanzu-yanzu: Gwamnatin tarayya ta gayyaci ma’aikata kan yajin aikin mafi karancin albashi

Gwamnatin tarayyar ta kara da cewa: “Saboda haka, titin Arterial Road N20 ne aka sanya wa sunan Farfesa Soyinka.  titin Murtala Mohammed kuwa ba a sauya masa suna ba, yana nan a yadda aka sanshi tun fil’azal”.

“Saboda haka muna kira ga daukacin al’ummar Najeria da su yi watsi da duk wasu jita-jita da ke nuna cewa an sauya sunan titin Murtala Mohammed, zuwa Wole Soyinka.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here