Zafin Rana: Kasar Saudiyya ta dakatar da Mahajjata daga jifan Shaidan na sa’o’i 5

Kasar, Saudiyya, Zafin, Rana, dakatar, Mahajjata, daga, jifan, Shaidan, sa'o'i
Ma'aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta dakatar da mahajjata zuwa gadar Jamarat domin gudanar da aikin jifa daga karfe 11 na safe zuwa karfe 4 na yamma...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta dakatar da mahajjata zuwa gadar Jamarat domin gudanar da aikin jifa daga karfe 11 na safe zuwa karfe 4 na yamma saboda tsananin zafin rana da ake fuskanta a kasar.

Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya, Dakta Abdulfattah bin Sulaiman, ne ya bayar da wannan umarni a cikin wata sanarwa a ranar Litinin a Mina, na Makkah, da ke Masarautar Saudiyya.

Ya ce matakan sun zama dole na ba da umarni don tabbatar da jindaɗin mahajjata domin yin aiki a saukake ba tare da fuskantar yanayin zafi ba.

Karin labari: ‘Yan Sanda sun gargadi masu tada zaune tsaye da yiwa tawagar sarki Sanusi ihu

“Saboda haka, an aiwatar da matakai kamar haka: An haramta wa maniyyata tafiya zuwa gadar Jamarat domin gudanar da aikin jifa daga karfe 11 na safe zuwa 4 na yamma.”

Ya ce za a jibge jami’an tsaro a sansanoni domin aiwatar da dokar hana duk wani mahajjaci tashi kafin karfe hudu na yamma.

Ya kuma bukaci ofishin al’amuran Hajji da masu ba da hidima da su tabbatar da bin doka da oda, inda ya kara da cewa za a dora musu alhakin duk wani laifin da aka aikata.

“Muna addu’ar Allah ya tsare maniyyata da kuma karban Hajjinsu” in ji Abdulfattah.

Karin labari: Eid-El-Kabir: Manyan wuraren shakatawa 10 da ake ziyarta a birnin Kano a lokutan bukukuwan Sallah

A halin da ake ciki kuma, jami’in hukumar alhazai ta Najeriya, ya kama wasu ‘yan Najeriya guda biyu Muhammad Umar, da Nazifi Tasi’u GARBA, bisa kutsawa cikin tantinan alhazai ba bisa ka’ida ba, sakamakon nuna damuwa dangane da karin masaukai da kuma kananan sata.

Don haka ne aka mika wadanda ake zargin ga hukumar ‘yan sandan kasar Saudiyya, inda aka samu na’urar tantance su, sannan aka ci tarar Riyal 10,000 a kan su biya duk lokacin da za su bar kasar.

NAN ta rawaito cewa Jamarat ginshikai ne guda uku da ke Makkah kuma muhimmin bangare ne na aikin Hajji ga Musulmi.

Karin labari: Yarjejeniyar tsagaita ɓude wuta ta kwanaki uku ta fara aiki a Sudan

A matsayin wani ɓangare na aikin hajjin su zuwa Makka, mahajjata suna jefa duwatsu a kan ginshiƙan don a alamance “jifan shaidan.”

Jifan Iblis-ko rajm al-jamarat, wanda aka fassara a matsayin jifa-hanyar da Musulmi za su yi watsi da jarabawa, da tabbatar da imaninsu ga Allah, da kuma girmama Annabi Ibrahim.

A cewar jaridar Saudi Gazette, sama da mahajjata miliyan 1.83 ne suka gudanar da aikin hajjin bana.

Alhazai 1,833,164 ne suka fito daga cikin Masarautar da kasashen waje domin gudanar da aikin hajjin shekara, kuma sun hada da mahajjatan kasashen waje 1,611,310 da mahajjata na cikin gida 221,854, ‘yan kasa da na kasashen waje kamar yadda NAN ta tattaro ta kuma tabbatar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here