
Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta nuna rashin jindadin ta game da ihun da wasu mutane suka yi wa tawagar Sarki Muhammadu Sanusi II yayin da yake komawa fadarsa bayan sallar Idi.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Kiyawa, ya fitar a ranar Litinin.
Ya ce, lamarin ya faru ne a lokacin da Sarkin ya bi wata hanya ta daban, a matsayin wani bangare na wajibcin addini.
Karin labari: Eid-El-Kabir: Manyan wuraren shakatawa 10 da ake ziyarta a birnin Kano a lokutan bukukuwan Sallah
Ya ce, abin takaici, wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun yi masa ihu a kusa da makarantar Firamare ta Festival da unguwar Zage da Zango.
“A halin yanzu, rundunar ‘yan sanda tana sa ido kan duk abubuwan da suka faru na Sallah don tabbatar da cewa an kiyaye doka da oda, an kuma samar da isassun matakan tsaro don dakile duk wata barazana ta tsaro.
Karin labari: Hukumar NUC Ta Amunce da duk kwasakwasan jami’ar tarayya ta Gombe
“Haka zalika, rundunar ‘yan sandan tana gargadin mutanen da ke da niyyar haifar da hargitsi ko rashin zaman lafiya a yayin bikin Sallah da su nisanta kansu daga jihar,” inji shi.
Kakakin ya ci gaba da cewa, a halin yanzu an tura isassun jami’an tsaro domin kame duk wani wanda ke yunkurin haifar da karya doka da oda.
Rundunar ‘yan sandan ta gargadi jama’a da su guji daukar makamai a lokacin bikin sallah da bayan bikin, inda ta ce duk wanda aka samu zai fuskanci hukunci mai tsauri.
Karin labari: YANZU-YANZU: Kotu ta tsige gwamnan Ebonyi da mataimakinsa daga kan mukamansu
“Aikin samar da tsaro na ci gaba da wanzuwa a dukkan kananan hukumomin da ke cikin jihar, domin tabbatar da an gudanar da bukukuwan sallah lami lafiya” in ji Kiyawa.