Gobarar kasuwa a Kano: Shettima ya sake tabbatar da kudirin gwamnatin tarayya na hana aukuwar haka a gaba

IMG 20260225 WA0001 750x430

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya sake tabbatar da kudirin gwamnatin tarayya na yin aiki tare da gwamnatin jihar Kano da hukumomin da abin ya shafa domin hana sake aukuwar gobara a kasuwannin jihar.

Ya bayar da tabbacin ne a ranar Laraba a Abuja lokacin da tawagar Kungiyar ‘Yan Kasuwar Kano karkashin jagorancin shugabanta, Alhaji Sabiu Bako, suka kai masa ziyarar godiya a Fadar Shugaban Kasa.

Ya bayyana cewa Ma’aikatar Jin Kai ta Kasa ta kammala dukkan takardun da suka dace domin fitar da Naira Biliyan Biyar da shugaban kasa ya yi alkawarin bayarwa don tallafawa ‘yan kasuwa da sauran wadanda gobarar ta shafa.

Ya ce shugaban kasa ya bayar da umarnin daukar matakan kariya tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar Kano domin kauce wa sake faruwar irin wannan gobara.

Ya kuma bayyana cewa adadin Naira Biliyan Biyar da aka amince da shi a matsayin tallafin gaggawa ya samo asali ne daga sakamakon kimantawar farko kan barnar da gobarar ta yi.

Shettima ya bukaci a gudanar da rabon da kuma amfani da kudaden cikin gaskiya da rikon amana, yana mai cewa gwamnati za ta hada kai da kungiyar ‘yan kasuwar domin samar da matakan kariya daga gobara don kare rayuka da dukiyoyi.

Ya kara da cewa tattalin arzikin kasa na kan turbar farfadowa, kuma gwamnati na da niyyar magance kalubalen masana’antu a Kano.

Ya yi nuni da aikin bututun iskar gas na Ajaokuta zuwa Kaduna zuwa Kano da kudinsa ya kai Dala Biliyan 2.8, wanda aka tsara domin samar da iskar gas a Arewacin Najeriya.

Ya ce aikin ya hada da tashar samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 1,350 a Kano, wadda aka kammala kusan kashi 80 cikin 100, domin farfado da masana’antu da karfafa wutar lantarki a jihar.

A nasa jawabin, Sabiu Bako ya roki gwamnatin tarayya da ta duba yiwuwar samar da rancen kudi mara ruwa ga ‘yan kasuwar da gobarar ta shafa, tare da ba su wa’adin biyan bashin har zuwa shekaru goma.

Ya kuma bukaci a ci gaba da tallafa wa sake gina muhimman ababen more rayuwa a kasuwar domin inganta tsaro da hana sake faruwar gobara.

Ya gode wa gwamnatin tarayya da kuma kungiyar gwamnonin APC bisa tallafin da suka bayar, yana mai cewa matakan da aka dauka cikin gaggawa sun taimaka wajen rage radadin asara da kuma farfado da fata a zukatan wadanda abin ya shafa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here