Babu Kasar Da Ta Taba Sauya Kudi A Lokacin Zabe Sai Najeriya —El-Rufai

El Rufai sabo
El Rufai sabo

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana cewar babu matsala a sauya fasalin takardun kudi, amma duk duniya babu kasar da ta taba sauyawa a lokacin zabe sai Najeriya.

El-Rufai ya yi zargin akwai gwamnan da shi kadai ya karbi sabbin kudi har na Naira miliyan 500 a kasar nan.

Ya bayyana hakan ne cikin wata hira da ya yi da sashen Hausa na BBC, inda ya ce an yi tsarin ne don masu kudi, amma da yawansu tsarin ba zai shafe su ba; zai kare ne a kan talaka.

“Babu laifi game da sauya kudi, kowace kasa na yi amma babu inda aka taba sauya kudi a lokacin zabe kuma aka bayar da wa’adi kadan, a ina aka taba yin haka a duniya?

“’Yan siyasa da manyan ’yan kasuwa da aka yi tsarin dominsu, suna da hanyoyin da za su samu kudin ba tare da sun wahala ba, wasu daga cikinsu su ke juya bankunan, amma wane hali talakawa da kananan ’yan kasuwa za su shiga?

“Duka gwamnonin APC sun gana a kan wannan matsalar, mun ga yadda mutane ke shan wahala, mun goyi bayan sauya kudi amma wa’adin da aka ware kamata ya yi a debi watanni.

“Mun bukaci CBN da gwamnoni da manajojin bankuna mu zauna don tattauna wannan matsalar domin mu yi aiki tare don warware wannan matsala, kamata ya yi a ce mun tsara yadda za mu bi mutane zuwa gidajensu, kauyukansu ba wai tilasta musu zuwa bankuna masu nisan kilomita don sauya kudadensu ba.

“Ina tabbatar muku wannan sauyin kudin bai shafi ’yan siyasa ba, saboda suna da kudi kuma suna da hanyar samun kudaden.

“Sun shirya sosai, talakawa ne kadai ba su san yadda za su samu kudin ba; ko a jiya an fada mana akwai gwamnan da shi kadai aka bai wa miliyan 500 na sabbin kudi,” in ji shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here