Atiku ya bawa ‘yan kasuwar kantin kwari tallafin naira miliyan 50 sakamakon iftila’in ambaliyar ruwan sama a kasuwar
Dantakarar shugabancin kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bawa ‘yan kasuwar kantin kwari tallafin miliyan 50 bisa ambaliyar ruwan sama da tai musu barna a kasuwar.
Jaridar Solacebase ta rawaitu cewa anyi mamakon ruwan sama a kwanakin da suka wuci, wanda harta kai ga ruwan yi yi ambaliya a wasu gurare da ke Kano, ciki harda kasuwar ta kantin kwari.
Atiku ya sanara da bada tallafin ne yau Litinin a gidan Malam Ibrahim Shekarau dake Mudunbawa a jihar Kano.













































