Majalisar Koli ta Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA) karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayyana cewa za a iya ci gaba da azumi a ranar Lahadi domin Najeriya ba ta ga wata ba, wanda hakan ke nuni da cikar watan Ramadan.
NSCIA ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakatarenta Farfesa Is-haq Oloyede, ranar Asabar.
Ya kuma bukaci al’ummar Musulmi da su nemi jinjirin watan Shawwal a ranar 29 ga watan Ramadan, yana mai jaddada cewa, “Idan Musulmi suka ga jinjirin wata bisa ga ka’idojin ganin watan, to mai martaba zai bayyana Lahadi 30 ga Maris, 2025 a matsayin 1 ga Shawwal da kuma ranar Idil Fitr.
Karin bayanai na nan tafe…..