An zabi Jaridar Solacebase da wasu 10 don asassa shirin bunkasa dabarun sadarwa karo na farko a Najeriya.

Solacebase Logo
Solacebase Logo

Fassarawa:Aminu Bala Madobi-Daga Kano

Asusun Haɓɓaka Zuba Jari a Kafafen Labarai ya sanar da zabar gidan jaridar Solacebase da wasu ƙungiyoyi 10 a matsayin rukunin farko da zasu shiga cikin shirin bunkasa sadarwar zamani a Najeriya.

Cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta ce an zabo wadanda suka yi nasara la’akari da irin aikace-aikace sama da 200 da aka duba bayan da kwamitin bada shawara da ya kunshi mashahurai da kwararru a aikin jarida, kasuwanci, ilimi da sabbin masana’antu.

Ta ce shirin na tsawon shekaru 3 zai yi aiki ne don karfafa aikin sadarwa dan samun hanyoyin tattara kudaden shiga masu dorewa da gina masu sauraron kafafen yada labarai masu zaman kansu a Najeriya, musamman wadanda ke isa ga al’ummomin da ba su da aiki.

“Asusun Ci gaban Jarida na Media Development Fund ne ke aiwatar da Shirin Kuma asusun saka hannun jari ne mai zaman kansa, wanda gidauniyar MacArthur ta ba da tallafi don haɓaka ƙirƙira da sabbin hanyoyin kasuwanci ga kafofin labarai masu zaman kansu a Najeriya.”

“Daga cikin Wadanda aka zabo su 11 dazasu halarcin gangamin suna daya daga cikin ƙungiyoyi waɗanda ke gina sabbin labarai da samfuran bayanai waɗanda ke bincika damar isa ga masu sauraro masu tarin yawa ta hanyar dandamalin zamani”

Gidajen sadarwar sun hadar da, Solacebase, Dubawa, HumAngle, TV 360, Jaridar mai kula da Al’adu, Resiyon manoma, Cibiyar binciken aikin jarida, Rediyon alumma ta Lavum, dakuma Prime Progress da Voix Collective.

Babban Daraktan Shirye-shiryen Asusun Haɓaka Zuba Jari na Media na Afirka Bilal Randeree, ya ce mahalarta taron za su ci gajiyar haɗin gwiwar tallafi, taimakon fasaha da dabarun haɓaka kwarewar aiki.

Idan za a iya tunawa, Jaridar Solacebase da wasu kungiyoyi 25 ne suka sami nasarar cin gajiyar tallafin kudade Haɗin gwiwa da Gidauniyar MacArthur a cikin 2022.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here