Allah ya yiwa ƙanin Dangote rasuwa

Sani Dangote 2
Sani Dangote 2

Allah ya yi wa ƙanin hamshaƙin attajirin Afrika kuma mataimakin shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Sani Dangote ya rasuwa.

Wata majiya daga dangin mamacin ce ta shaida wa jaridar Solacebase cewa haiƙin ɗan kasuwar ya rasu ne bayan fama da jinya a wani asibitin ƙasar Amurka jiya Lahadi.

Majiyar ta ce, an shirya yadda za a dawo da gawarsa Najeriya domin yin jana’iza.

Marigayin ya kasance hamshaƙin ɗan kasuwa mai zuba jari a muhimman sassa na tattalin arziki da suka haɗa da masana’antu da hrkokin noma da na bankuna da kuma harkokin mai.

Ya kuma zauna a hukumar wasu kamfanoni da suka haɗa da Nigerian Textile Mills Plc Nutra Sweet Limited Gum Arabic Limited da Dangote Textile Mills Limited da Alsan Insurance Brokers Dan-Hydro Company Limited Dansa Food Processing Company Limited da kuma Dangote Farms Limited.

Ya kuma Taɓa zama mataimakin shugaban kungiyar masu sana’ar sarrafa ƙaro ta Afirka sannan kuma ya taɓa zama shugaban kungiyar kwallon Polo na Legas sau biyu baya ga kasancewarsa ƙwararren ɗan wasan Polo.

Har ila yau, ya kasance mamba a cibiyar ƙwararrun masu shige da ficen kayayyaki ta jiragen ruwa watau Fellow of Chartered Institute of Shipping of Nigeria kuma Shugaban ƙungiyar masu samar da takin zamani ta FERSAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here