Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia ya ce adadin waɗanda suka mutu a harin da wasu ƴanbindiga suka kai ƙananan hukumomin Ukum da Logo a jihar ya kai 56.
Yayin da yake jawabi ga manema labarai bayan ya ziyarci garuruwan, Mista Alia ya bayyana harin da na jahilci da rashin imani.
”A yanzu da nake jawabi, mutum 56 ne suka mutu waɗanda ba su ji ba su gani ba, da suka haɗa da iyaye da maza da mata da ƙananan yara”, in ji shi.
Gwamnan ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta gaggauta ɗaukar matakai domin kawo ƙarshen hare-hare a jihar.
”Al’ummarmu na da haƙƙin rayuwa cikin kwanciyar hankali, su yi noma su taso cikin iyalansu su reni ƴaƴansu ba tare da wata fargaba ba”, kamar yadda ya bayyana.
Gwamnan ya ce ya gana da shugabannin al’umma da mutanen da harin ya shafa, inda ya saurari kokensu, tare da tabbatar musu cewa gwamnatin jihar na tare da su, ba za ta taɓa yin watsi da su ba.
Mista Alia ya ce tuni gwamnatin jihar ta ƙara tura jami’an tsaro zuwa yankunan domin kwantar da hankula.
Harin na zuwa ne kimanin mako biyu bayan wasu ƴanbindiga sun kashe fiye da mutum 100 a wasu hare-hare a jihar Plateau mai makwabtaka.
BBC